Bangaren siyasa da zamantakewa; an cimma matsaya guda da sanyawa wata yarjeniyar fahimtar juna a tsakanin jami'o'I biyu na musulunci wato jami'ar musulunci ta Imam Abu Hanifa a kasar Tajikistan da kuma jami'ar musulunci ta Kazan a kasar Tataristan.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an cimma matsaya guda da sanyawa wata yarjeniyar fahimtar juna a tsakanin jami'o'I biyu na musulunci wato jami'ar musulunci ta Imam Abu Hanifa a kasar Tajikistan da kuma jami'ar musulunci ta Kazan a kasar Tataristan.Wannan yarjeniya da fahimtar juna a tsakanin jami'o'in biyu Abdul Mana Said Uf shugaban bangaren nazari da kula da hulda da jama'a a jami'ar musulunci ta Tajikistan ne ya sa hannu yayin da Rafik Muhammad Shin shugaban jami'ar musulunci ta Kazan ya sa hannu.Yarjejeniya ta kumshi harakar ilimi da fada wannan fanni na koyarwa a tsakanin jami'o'in biyu.
924453