IQNA

Taro Kan Musulunci Da Musulmi Masu Tsautsauran Ra'ayin Addini A Faransa

Bangaren kasa da kasa: a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa ne za a gudanar da taron a ranar asabar goma sha bakwai ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku hijira shansiya taron da zai yi nazari da dubi kan addinin musulunci da kuma masu ra'ayin addini da riko da shi da kuma masu tsananin ra'ayin addini.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa ne za a gudanar da taron a ranar asabar goma sha bakwai ga watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku hijira shansiya taron da zai yi nazari da dubi kan addinin musulunci da kuma masu ra'ayin addini da riko da shi da kuma masu tsananin ra'ayin addini.Wannan babbar mu'assisar yin nazarin a yankin Medetariya da yankin gabas ta tsakiya net a shirya da kuma za a samu halartar yan jami'a da malamansu da suka fito daga jami'o'I daban daban kuma da dama da za su halarci wannan taro da bayyana ra'ayoyinsui da kuma irin nazari da bahasin da za su bayar kan wannan lamari da yadda za a shawo kan matsalolin da ake fuskanta da masu tsananin ra'ayin addini da ke gogawa sauran musulmi a duniya kashin kaji da taimakawa wajan fakewa ana nuna masu karan tsanani a Duniya.

926476