IQNA

An Gina Masallacin Farko A Janva A Kasar Italiya

Bangaren siyasa da zamantakewa; shugabanni da wakilai da suka halarci zaman magadin gari na Janva da ke yankin Liguriya na kasar Italiya sun amince da shawarar gina masallacin farko na musulmin wannan gari.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; shugabanni da wakilai da suka halarci zaman magadin gari na Janva da ke yankin Liguriya na kasar Italiya sun amince da shawarar gina masallacin farko na musulmin wannan gari.Sai dai a daidai lokacin da musulmin wannan garin ke murna da jin dadin wannan mataki da mahukumtan garin suka dauka na amince da gina wannan masallacin sai gashi wakilin jam'iyar mai zaman kanta da nuna banbancin launin fata ta Hadin kan arewaci ya soki lamarin matakin da mahukumtan kasar suka dauka da cewa ba za ta sabu ba da kara cewa; bad a jimawa ba muka yi mazauna wannan gari alkawali dab a su tabbacin ba za gina wani masallaci a wannan gari ba amma sai gashi magajin garin Janava ya amince da shirin gina masallaci a wannan gari.

928980