Bangaren adabi :shugaban kamfanin ta'awuni da wallafa littafai a birnin Qum ya bada sanarwa da labarin gudanar da wata kasuwar baje kolinlittafe na musamman na addini da Mazhabobi daga ranar ashirin da biyu zuwa ashirin da bakwa na watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Qum.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; shugaban kamfanin ta'awuni da wallafa littafai a birnin Qum ya bada sanarwa da labarin gudanar da wata kasuwar baje kolinlittafe na musamman na addini da Mazhabobi daga ranar ashirin da biyu zuwa ashirin da bakwa na watan Dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Qum. Said Mahmud Huseini a wata tattaunawa da ta hada shi da kamfanin dillancin labaran Kur'ani na Ikna ya yi nuni da gudanar da wannan kasuwar baje kolin littafen musamman na addini da cewa: kasuwar baje kolin littafen addini kaso na biyu da kungiyar hadin kan marubuta ta shirya a birnin Qum tare da hadin guiwar ofishin da ke kula da harkokin al'adu a ma'aikatar al'adu da fadakarwa ta Musulunci da kuma ofishin kula da duk wata harka ta al'adu a lardin Qum sun amince da gudanar da wannan kasuwar baje kolin littafe daga ranar ashirin da biyu zuwa ashirin da bakwai na watan Dai na wannan shekara kuma masu buga littafe na cikin gida da na ketare da dama ne za su halarci wannan kasuwar baje kolin da suka fito daga kasashen larabawa da na musulmi kamar kasashen Labanon,Masar da Iraki.
929072