IQNA

Kai wa Guraren Ibada Na musulmi Hari Ta'addanci Ne Kan Bil Adama

Bangaren kasa da kasa: Cibiyar kula da harkoki da dangantaka ta al'ummomi a kasar Kanada FCRR a jiya sha takwas ga watan dai na shekra ta dubu daya da dari uku da tis'in hijra shamsiya ta bukaci rundunar yan sandan kasar da ta sanya kai wa guraren ibada da kai hare hare kan musulmi da addinin musulunci a matsayin wuce gonad a iri da ta'addanci kan bil adam.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsari a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Cibiyar kula da harkoki da dangantaka ta al'ummomi a kasar Kanada FCRR a jiya sha takwas ga watan dai na shekra ta dubu daya da dari uku da tis'in hijra shamsiya ta bukaci rundunar yan sandan kasar da ta sanya kai wa guraren ibada da kai hare hare kan musulmi da addinin musulunci a matsayin wuce gonad a iri da ta'addanci kan bil adam.A cikin bayanin da ta yi cibiyar ta bayyana cewa; tana yin Allah wadai da tofin Allah tsine da ake kai wa masallatai da cibiyoyin ibada na musulmi kuma irin kai wadannan hare haren ta'addanci na tayar da hankalin al'ummar kasar kanada kuma suna kiran da aka kawo karshen kai irin wadannan hare haren wuce gonad a kuma takalar fada da tada fitini a tsakanin al'umma.
930792