Bangaren al'adu da fasaha; shugaban hukumar kula da al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a ketare da kuma dangantaka a tsakanin musulmi a lokacin wata ziyarar aiki a kasar Tanzaniya ya bayyana cewa: za su fadada wakilansu masu yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a nahiyoyi domin kara kusanci a tsakanin mabiya sauran addinai da kabilu.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ta watsa rahoton cewa: shugaban hukumar kula da al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a ketare da kuma dangantaka a tsakanin musulmi a lokacin wata ziyarar aiki a kasar Tanzaniya ya bayyana cewa: za su fadada wakilansu masu yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a nahiyoyi domin kara kusanci a tsakanin mabiya sauran addinai da kabilu.A ranar sha bakwai ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in ne Khuramshad shugaban hukumar yada al'adun jamhuriyar musulunci a ketare ya bayyana cewa; ssuna kokarin ganin sun kara yawan wakilansu a kasashen waje masu yada al'adun Iran a ketare daga tamanin zuwa dari da kuma za su aika su zuwa kasashen Afrika da latin Amerika.Wannan bayanin nasa na nuni da yadda jamhuriyar musulunci ke bada muhimmanci a kara habaka dangantakarta da sauran kasashen duniya da kara kusanci na addini da al'adu.
931603