Bangaren siyasa da zamantakewa: taron karawa juna sani da ilimi na addini da ilimi mai taken Imam Huseini (AS) da kuma hadin kai da tsama tsintsiya guda tsakanin al'ummar musulmi da aka gudanar a ranar sha takwas ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a lardin Hirat na jamhuriyar musulunci ta Afganistan.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ta watsa rahoton cewa: taron karawa juna sani da ilimi na addini da ilimi mai taken Imam Huseini (AS) da kuma hadin kai da tsama tsintsiya guda tsakanin al'ummar musulmi da aka gudanar a ranar sha takwas ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a lardin Hirat na jamhuriyar musulunci ta Afganistan.Wannan taron karawa juna sani an samu halartar mutane da daman gaske day a hada fitattun yan siyasa da shugabannin al'adu da zamnatakewa da malaman addini a wannan lardin domin samar da wani yanayi na hadin kai a tsakanin musulmi baki daya ba tare da la'akari da shi'a ne ko sunna .Irin wannan taro ko ba komi yana da muhimmancin wajan kara kusanci da hadin kai a tsakanin musulmi musamman a daidai wannan lokaci da kulka makirci da kokarin raba kan musulmi ke kara fadada da kai wa juna hare hare a wasu yankuna da kasashe a makrci kawo sabani da rabuwar kawuna a tsakanin musulmi.
932062