Bangaren kasa da kasa : an baje kasuwar baje kolin abubuwan fasaha domin taimakawa al'ummar da ake zalunta a kasar Bahrain a daidai lokacin gudanar da taron cika kwanaki arba'in da shahadar imam Huseini (AS) da yan jami'a Iraniyawa a garin Karbala suka gudanar.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an baje kasuwar baje kolin abubuwan fasaha domin taimakawa al'ummar da ake zalunta a kasar Bahrain a daidai lokacin gudanar da taron cika kwanaki arba'in da shahadar imam Huseini (AS) da yan jami'a Iraniyawa a garin Karbala suka gudanar.Wannan kasuwar baje kolin ta fasaha an nuna hotuna da zanen yadda jami'an tsaro a kasar baharain tare da hadin guiwar jami'anb tsaron Saudiya da aka dauko hayarsu ke aiwatar da ayyukan ta'addanci da kisan kiyashi kan fararen hula masu neman kawo canji da sauye-sauye a kasar ta Bahrain l.Wannan ya fito da zalunci da nanniya da rashin tausayin fararen hula na kasar Ta Bahrain da shugabanni da mahukumtan kasar suke nunawa da kuma suka jima suna aiwatarwa a cikin kasar.
934463