Bangaren kasa da kasa: Hukumar da ke kula da hulda da dangantaka a tsakanin musulmi a ranar ashirin da shida ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da marece ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta ke yin Allah wadai da tofin Allah tsine da harin ta'addanci da rashin tausayi da aka kai wa tawagar masu ziyarar juyayin cika kwanaki arba'in da zagayowar ranar shahadar Imam Huseini (AS) a garin Basra.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; Hukumar da ke kula da hulda da dangantaka a tsakanin musulmi a ranar ashirin da shida ga watan dai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da marece ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta ke yin Allah wadai da tofin Allah tsine da harin ta'addanci da rashin tausayi da aka kai wa tawagar masu ziyarar juyayin cika kwanaki arba'in da zagayowar ranar shahadar Imam Huseini (AS) a garin Basra.Ikmalul Dine Ihsan Uglo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya fitar da wannan sanarwa da a cikinta da kaukausar murya yake yin Allah wadai da tofin Allah tsine kan wannan harin ta'addanci da aka kai da wani abu mai fashewa day a yi sanadiyar kisa da jikkata mutane da dama fararen hula .Kuma a wanni bangare ya gayyaci dukan bangarori na Iraki day a hada yan siya da malaman addini a Iraki das u bi hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a wannan kasa da hada kai da kawo karshen sabani da banbance a tsakaninsu.Kuma kai hare haren ta'addanci wani kokari ne na rarraba da kawo fitina a tsakanin al'ummar Iraki.
936506