IQNA

Taron Karawa juna Sani Mai taken Muhammadu manzon Allah (SWA)) A Faransa

Bangaren kasa da kasa: taron karawa juna sani mai taken Muhammadu ma'aikin Allah tsira da amincin allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkakka da za a fara a yau sha shidda ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a babban masallacin garin Liyon na Faransa.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; taron karawa juna sani mai taken Muhammadu ma'aikin Allah tsira da amincin allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkakka da za a fara a yau sha shidda ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a babban masallacin garin Liyon na Faransa.Wannan taron karawa juna sani ana gudanar das hi ne a daidai lokaci guda na tunawa da zagayowar ranar haifuwar fiyayyan halitta manzon allah Muhammadu dan Abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka kuma za a fara bayan an yi sallar laasar a babban masallacin birnin na Liyon kuma makarancin kur'ani Abdul Aziz Abu Bakir ne zai farad a karanto ayoyin kur'ani mai girma sai kuma malamai dam asana musulmi da manyan baki a kasar Faransa su gabatar da jawabai da yin dubi a cikin tarihin rayuwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka. Kuma an gayyaci musulmi da wadanda ba musulmi ba domin kollon fim ta Muhammadu Manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka da kuma sauraren jawaban da malamai za su yi.
946721