IQNA

Gangamin Nuna Adawa Da Matakin Hana Sanya Hijabi A Makarantu A kasar Keniya

Bangaren siyasa da zamantakewa; yan makaranta a mata a kasar Keniya a daidai lokacin da wata makaranta a birnin Nairobi fadar mulkin kasar ta hana wa mata da ke karatu a makarantar sanya hijibi sun yi taron gangami a gaban daya daga cikin kotunan birnin domin nuna adawarsu a fili karara da wannan mataki na nuna banbanci da zalunci.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: yan makaranta a mata a kasar Keniya a daidai lokacin da wata makaranta a birnin Nairobi fadar mulkin kasar ta hana wa mata da ke karatu a makarantar sanya hijibi sun yi taron gangami a gaban daya daga cikin kotunan birnin domin nuna adawarsu a fili karara da wannan mataki na nuna banbanci da zalunci. Yan makarantar mata da aka takewa hakkinsu na sanya hijibi da sauran takwarorinsu na sauran makarantu da kuma uwayensu ne suka halarci wannan gagaramin taron gangami na nuna adawrsu da wannan mataki na nuna wariya da banbanci a tsakanin yan kasar ta Keniya da dora ayar tambayar sanin dalilin da ake nuna masu wannan banbanci da takura masu ta fuskar addini'zamnatakewa da kuma al'adu . Har ila yau sun bayyana ce makarantun da ke daukan irin wannan mataki sun sabawa dokokin ma;aiaktar da ke kula da harkokin karatu da kundin tsarin mulkin kasar ta Keniya.
948620