Bangaren siyasa da zamantakewa; a wani taron kasa da kasa na karawa juna sani a jami'ar muslmin a yankin Urdu Bagh a garin Aligar da ke lardin Urtarparadesh na kasar Indiya za a gudanar da bincike na nazari kan sirri da matsayin Irfani a addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a wani taron kasa da kasa na karawa juna sani a jami'ar muslmin a yankin Urdu Bagh a garin Aligar da ke lardin Urtarparadesh na kasar Indiya za a gudanar da bincike na nazari kan sirri da matsayin Irfani a addinin musulunci. Wannan taron kasa da kasa na karawa juna sani kan Irfani a musulunci da aka fara a ranar sha tara ga watan Bahmai na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in za a kwashe kwanaki uku ana gudanar das hi da malamai da Manawa da kwararru kan wannan fanni za su yi nazari da bincike da masanyar ra'ayi domin gano sirrin da ke tattare da wannan fanni na Irfani.An bude wannan taro ne da karatun wasu ayoyin kur'ani mai girma da kuma zikiri da ambatonm Allah da kuma yabo da wasu malaman jami'a da suka halarci wannan taro suka karanto.
950155