Bangaren fikira, malamin jami’a kuma malamin Hauza ya bayyana cewa mahangar masu ikirarin bin sabon tafarkin irfani, ya zama wajibi kansu su san cewa dukkanin abin da mutum zai dogara da shi ta wannan fuska dole ne ya ginu kan mahangar addini sahihiya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hojjatul Islam Dr. Mu’ahhad Taqi Fali ya sheda cewa malamin jami’a kuma malamin Hauza ya bayyana cewa mahangar masu ikirarin bin sabon tafarkin irfani, ya zama wajibi kansu su san cewa dukkanin abin da mutum zai dogara da shi ta wannan fuska dole ne ya ginu kan sahihiyar mahangar addini.
Ana bada muhimmanci na musaman ga iyalan gidan manzo tare da jaddadawa game da ziyarar manzon rahama (saww) da kuma Imam Ali da Imam Hussaini (AS) har ila yau da kuma jaddadawa game da ziyarar kabrurrukan A'imma baki daya, kamar dai yadda muka ambata a sauran ruwayoyi da muka kawo a farkon wannan babi a bayanin da muka yi karkashin (ziyarar kabarinsu) mun kawo ruwayoyi masu yawa dake karfafa wannan ma'ana, kuma a nan ma zamu yi nuni da wasu daga cikin su da suke karfafawa game da wannan ma'anar.
An ruwaito daga zaid dan shahham yace "( wata rana na cewa Abi Abadullah (as ) wace irin falala ce ke ga wanda ya ziyarci Imam Hussain (AS) ? sai ya ce: falalarsa kamar wanda ya ziyarci Allah ne a Al'arshinsa. Ya ce sai na ce: to wace irin lada ce ke tattare da wanda ya ziyarci daya daga cikin ku sai ya ce: kamar wanda ya ziyarci manzon Allah ne (saww)
An karbo daga Isa bin Rashid ya ce : na tambayi Aba Abdullah: nace raina fansarka. wacce falalla ce ke tattare da wanda ya ziyarci kabarin Imam Husaini (AS) kuma ya yi sallah raka'a biyu a wurin? : sai ya ce Allah zai rubuta masa ladan wanda ya yi aikin hajji da umra ya ce sai nace; raina fansarka ya dan manzon Allah, haka ma dukkan wanada ya ziyarci Imami da aka wajabta mana yi masa da'a daga cikin iyalan gidan manzo? Sai yace : haka yake ga dukkan wanda ya ziyarci kabarin Imami daga cikin iyalan manzo da aka lizimta yi musu da'a ko kuma biyayya.
An karbo daga Abdurrahman bin Muslim ya ce: "wata rana na shiga wurin Imam Kazim (as) sai nace masa; wanne yafi falala, ziyarar Amirul Mua'minin Ali (as) ko kuma ziyarar Abi abdallah (As ) da ma sauran dukkan Immai, kuma na ambaci sunansu daya bayan daya. Sai ya ce min: ya kai Abdurrahman dan muslim duk wanda ya ziyarci na farkonmu, to fa tamkar ya ziyarci na karshenmu ne, haka ma wanda ya ziyarci na karshenmu to fa tamkar ya ziyarci na farkonmu ne, duk wanda ya mika wila'a ga na farkonmu kamar ya mikata ne ga na karshenmu, haka ma wanda ya mika ta ga na karshenmu, kamar ya mika ta ne ga na farkonmu, haka kuma duk wanda ya biya bukatar daya daga cikin masoyanmu to kamar ya biya dukkan bukatunmu ne, ya kai Abdurrahman ka so mu, ka so wanda yake son mu, kuma ka yi soyayya don mu, ka mika wiliya gare mu ga kuma wanda ya mika wilayara gare mu, kuma kaki wanda ya yi kiyayya da mu, ka sani cewar yin musu gare mu tamkar yin musun manzo ne da kuma kakanmu Ali (as)
Kamar ya yi musu ga Manzon Allah (saww) ne wanda ya yi musun Manzon Allah (SAWW) hakika ya yi musun Allah Madaukakin sarki ne. Ka sani ya Abdurrahman duk wanda ya yi gaba da mu hakika ya yi gaba kai tsaye da manzo Allah ne, kuma duk wanda ya yi gaba da Manzo hakika ya yi gaba da Allah madaukakin sarki ne, kuma duk wanda ya yi gaba da Allah madauakakin sarki to hakki ne akan Allah ya sanya wuta ta zama ita ce makomarsa, kuma ba shi da wani mataimaki."
Kari a kan wannan akwai wasu ruwayoyi da suka yi bayani sosai game da falalar ziyarar ko wanne daya daga cikin iyalan gidan manzo wadanda Allah ya tsarkake su daga dukkanin najasa da dauda, kuma mun riga mun ambata a cikin ziyarar manzo wasu nassoshi da suke da alaka da kabururukan A’imma da suke Baki'a tsira da Amince ya tabbata gare su, to a nan ma za mu yi ishara ga wasu nassoshin na daban.
An rawaito daga mohammad bin Ahmad bin Dawud daga dan sinan ya ce: na ce wa Imam Ridha (AS) wace irin lada ce ke ga wanda ya ziyarci mahaifinka? sai ya ce: Aljannah na jiransa.
Ya zo a cikin wata ziyara daban da aka karbo daga zakariya bin Adam Al ‘kummi daga Imam ridha (AS) ya ce: lallai Allah ya tseratar da birnin Bagadaza da wurin da kyawawa biyu suke a cikinta.
Haka ma kamar yadda yazo a wasu ruwayoyi da dama cewar lallai ziyarar kabarin Imam Musa bin Ja'afar (AsS tamkar ziyarar kabarin Imam Husssaini (AS) ne.
Ya zo a cikin wata ziyara daban cewar lallai ziyarar sa tamkar ziyarar manzon Allah ne da kuma kabarin Amirul mu'aminina Ali (as) sai dai na manzo da Imam Ali su ne suka fi falala sosai. Kamar yadda yazo a cikin ruwayoyi masu yawa da wasu suka amince da su game da falalar ziyarar Aliyu bin Musa Ridha (as) zamu fadi wasu daga cikin su kamar haka.
An karbo daga Ja'afar bin Mohammd bin Ammara, daga babansa daga Sadiq (as) daga mahaifansa (as) yace: manzon Allah ya ce za a bizne wata tsoka daga jikina a kasar khurasan babu wani Mu'amini da zai ziyarce shi face Allah.
yazo a cikin wata ruwaya daga Imam Ridha (As) yana cewa: babu wani daga cikin mu face wanda aka kashe shi ta hanyar yin shahada sai aka ce masa ya jikan Manzon! Allah waye zai kashe ka, sai yace mafi sharrin halittar Allah a zamanina zai kashe ni ta hanyar ba ni guba in sha, sannan za a bizne ni a wani gida kuntatacce, kuma a wani gari da ni bako ne a cikinsa, ku sani ! duk wanda ya ziyarce ni duk da nisan da nake da shi, Allah madaukaki zai rubuta masa ladan shaidai dubu dari, da kuma kwatankwacin ladan siddikai dubu dari, da kuma ladan mahajjata da umara dubu dari, da kuma mujahidai dubu dari, kuma za a tashe shi a karkashin inuwarmu, kuma zai zama makwabcinmu a cikin Aljannah madaukakiya."
A cikin wata ruwaya da aka ruwaito ta daga Amirul mu'aminina (as) ya ce: Manzon (saww) ya ce za a bizne wata tsokar jikina a kasar khurasan, babu wani mutum dake cike da bakin ciki da zai ziyarce ta face Allah ya yaye masa bakin cikinsa, ko kuma mai zunubi face Allah ya gafarta masa zunubansa."
Amma sauran A’imma duk da yake ba a kawo wasu ruwayoyi da sukayi magana musamman akan falalolin ziyarar su ba, banda sauran nassoshin da muka kawo da sukayi magana a kan ziyarrasu baki daya da ko kuma suka yi ishara a kansu , ko kuma wasu sashin ruwayoyi da basu da yawa misali kamar wandda yazo acikin ruwayar Imam Hassan Askari ( as) inda yake cewa kabari na a Sirri man Ra'a, aminci ne ga ma'abota bangarori ko kuma wani nassi da Imam Al’hadi (AS) ya fadi wata addu'a daya koyawa wani daga cikin Sahabbansa inda a ciki yake cewar hakika na roki ubangiji da kada ya kunyata wanda ya yi addu'a a gaban kabari na."
ku kuma wata ruwaya da aka sanyawa hannu da Mohammad bn Himiyari ya fito dashi daga Imamul Hujja (As) wanda acikinta yake fadan yadda ake ziyararsa (as) da dai sauran irin wadannan bayanai da basu da yawa , sai dai dogara da irin wanam afili yake saboda yawan ruwayoyin da suka zo game da wannan batu da kuma jaddadawar da aka yi a dunkule da kuma kebance.
926003