Bangaren al’adu da fasaha, marigayi Imam Khomeni (RA) wanda ya jagoranci kafa jamhuriyar muslunci ta Iran ya bi sahihin tafarki ne na koyarwar addinin da manzon allah ya zo da shi shi ya samu babban taimako daga Allah madaukakin sarki wajen isa zuwa ga manufarsa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wasu daga cikin masana da malaman addinin sun ammanar cewa fasaha, marigayi Imam Khomeni (RA) wanda ya jagoranci kafa jamhuriyar muslunci ta Iran ya bi sahihin tafarki ne na koyarwar addinin da manzon allah ya zo da shi shi ya samu babban taimako daga Allah madaukakin sarki wajen isa zuwa ga manufarsa domin tabbatar da wannan adini da tsarinsa a cikin ‘yan adam.
A yayin da ya ke gabatar da jawabinsa a lokacin ganawar, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana yunkurin al'ummomin kasashen musulmi na kifar da shugabannin kama-karya ‘yan amshin shatan manyan kasashen duniya a matsayin lamari mai matukar muhimmanci sannan kuma wani mafari na yunkurin ganin bayan lalatattun cibiyoyin yahudawan sahyoniya da ma'abota girman kan duniya. Jagoran ya ci gaba da cewa: Sakamakon wannan yunkuri mai cike da albarka, da yardar Allah al'ummar musulmi za su sake dawo da daukaka, ‘yanci da kuma tsayin dakan da suke shi a baya.
Ayatullah Khamenei ya bayyana matasan kasashen musulmin a matsayin masu dauke da babbar bishara ga makomar al'ummar musulmi, daga nan sai ya ce: Farkawar da matasan kasashen musulmi suka yi, lamari ne da ke kara irin fatan da ake da shi na farkawar dukkanin al'ummar musulmi na duniya.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa a halin yanzu tarihin bil'adama yana fuskantar wani gagarumin sauyi mai girma ne, daga nan sai ya ce: Bil'adama dai sun gwada dukkanin akidu na abin duniya da suka hada da gurguzu, jari hujja, ‘yan kasanci da rashin yarda da Ubangiji, to amma a halin yanzu suna a wani sabon yanayi ne wanda babbar alamar hakan ita ce irin yadda al'ummomi suka koma ga Allah Madaukakin Sarki da kuma neman taimako daga wajen karfi maras karewa na Ubangiji da kuma dogaro da koyarwar Ubangiji.
Haka nan kuma yayin da ya ke ishara da irin yadda gungun ‘yan kama karya da kuma lalatattun yahudawan sahyoniya da sauran ma'abota girman kan duniya suke juya duniya yadda suke so, Jagoran cewa ya yi: Yunkurin al'ummomin wannan yankin wajen tinkarar lalatattun ‘yan kama-karya wani bangare ne na gwagwarmayar bil'adama da mulkin kama-karyar yahudawan sahyoniya, sannan kuma bayan wani yanayi mai girma na tarihi, bil'adama za su tsira da wannan kama-karya mai tsananin hatsari. Ko shakka babu wannan sauyi mai girma da ke faruwa tabbaci ne na alkawarin Ubangiji na ‘yantar da al'ummomi (daga mulkin ‘yan kama-karya) da kuma tabbatar da iko na koyarwar Ubangiji.
955257