Bangaren kasa da kasa, a koda yaushe irfani yana tafiya ne bisa koyarwar ta masana wannan fagen kuma babbar manufarsa ita ce isa zuwa ga Allah ta hanyar mayar da komai zuwa gare shi, tare da mika wuya kai tsaye ga mahaliccin kowa da komai ta hanyar tarbiyantar da ruhi kan bin Allah.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hoj. Eslam Dr. Muhammad Taqi Fali malamin jami’a da kuma cibiyar ilimi da bincike kan ilmomin addinin muslunci ta Hauza ya sheda cewa, koda yaushe irfani yana tafiya ne bisa koyarwar ta masana wannan fagen kuma babbar manufarsa ita ce isa zuwa ga Allah ta hanyar mayar da komai zuwa gare shi, tare da mika wuya kai tsaye ga mahaliccin kowa da komai ta hanyar tarbiyantar da ruhi kan bin ubangiji mai girma da daukaka.
Ranar juma'a da darenta suna da wani fifiko da daraja na musamman fiye da sauran kwanaki da darare. Kamar yadda ya zo a cikin hadisan Ahlul baiti (as) inda aka siffanta ta da cewa ranace da Allah yake ‘yanta bayinsa guda dubu sittin daga shiga wuta a cikin kowace sa'a daga cikin sa'oin ranar, haka kuma Allah yana rubanya lada ninkin banikin kuma yana shafe muna nan ayyukan mutum kuma yana daga darajojin mutane yana biyan bukatun su, tare da yaye musu duk wani bakin ciki, kuma yana amsa addu'oi, yana gafarta zunubai, kuma yana karbar tuba, yana saukar da arziki, kuma Allah yana daukar fansar wanda aka zalunta a kan azzalumi. To yanzu bari mu yi ishara game da wasu ruwayoyi uku da suka zo kan wannan batun.
An karbo daga Imam Ridha ya ce: Manzon Allah ya ce: Lallai ranar Juma'a ita ce shugaban ranaku domin kuwa a cikinta Allah yakan rubanya ladan kyawawan ayyuka, kuma yana shafe muanana ayyuka, yana daukaka darajoji, tare da amsa Adduo'i, a cikinta yana yaye bakin ciki, yana biyan manyan bukatu, ita ce ranar da Allah yake kara yawan wadanda zai yanta daga wuta, babu wani mutum da zai yi addu'a a cikinta yana masani da hakkinta da harmcinta, face ya kasance hakki ne a kan Allah ya sanya shi cikin jerin wadanda zai yanta daga wuta, inda da zai mutu a cikin wannan daren ko kuma da rana daya mutu shahidi kuma za a tashe shi yana mai imani, babu wanda zai yi kasa a gwiwa game da haramcinsa da kuma tozarta hakkinsa face ya kasance hakki ne a kan Allah ya sanya shi a wutar jahannama sai dai in ya tuba.
An karbo daga Imam Bakir cewa: "babu wata rana da za ta fito a cikin kowacce rana da za ta fi ta ranar juma'a, domin kuwa hatta ma tsuntsaye idan sashinsu ya hadu da sa shi maganarsu ita ce aminci rana ta gari."
An karbo daga Imam Sadiq ya ce: duk wanda ya samu kansa a ranar juma'a to kada ya shagaltar da kansa da komai bayan ibada, domin a cikin ranar ana gafarta wa bayi kuma ana saukar musu da rahama."
Ya wajaba a yi salla a ranar juma'a bisa cikakken bayanan da malamai Suka yi a littafan fikihu, kari a kan wanann za mu ga akwai wasu ayyuka da mustahabbai da ke cikin wadannan darare da ranaku da ya kamata mu Samu cikakken bayani a kansu a cikin littatafan Addu'oi da ayyuka, sai dai za mu yi shinfida game da wannan kamar haka:
Wanka a ranar juma'a, hakika an jaddada game da mustabancin yin sa, duk da yake cewa wasu malamai ma sun nuna wajibcinsa.
Karanta Al'kur'ani musamman ma suratul Rahman, da Ahkaf da kuma Mu'minun, da suratul waki’a.
Ciyarwa da yin Sadaqa da kuma kyautatawa musamaman ma ga iyali da da makusanta dangi, Sanya tufafi masu kyau da kuma gyara jiki da fesa turare mai kamshi a ranar ta juma'a, yawaita yin sallah ta musamman misali kamar sallar manzo da Ali da Fatima da kuma Sallar Ja'afaru Tayyar (Alihimus salam) haka zalika ya waita yin Salati ga manzo da iyalan gidansa.
Yawan karanta adduo'i da zikirori musamman zababbu, misali Addu'ar kumail, da kuma addu'ar "man tahayya'a wata'aba'a" da kuma addu'ar" ya shahidi kulli najwa" wato ya wanda yake sane da dukkan sane wata ganawa, da kuma addu'ar Imam Aliyu bin Hussain a ranar juma'a da kuma addu'ar Satmat, da sauran adduo'i daban-daban, haka ma tasbihan nan guda hudu, wato tasbihul arba'a. da dai wasu da dama daga cikin zikirori.
Karanta ziyarar Imam Hussain a daren Juma'a, da ziyarar manzo da ziyarar A’imma da kuma ziyarar kabarurruka a safiyar ranar juma'a, da kuma ziyarar yan'uwa, bada muhimmanci ga koyon mas’alolin addini da kuma hukumce-hukumcen shari'a.
916753