Bangaren kasa da kasa: hukumar da ke kula da ilimi da al'adun musulunci ta Asesko da ke karkashin kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar juma'a biyar ga watan Isfand shekara ta dbu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta fitar da wani bayani na yin Allah wadai da hare haren ta'addancin baya bayan nan da aka kai wa garuruwa daban daban a Iraki a ranar alhamis hudu ga watan na Isfand.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: hukumar da ke kula da ilimi da al'adun musulunci ta Asesko da ke karkashin kungiyar hadin kan kasashen musulmi a ranar juma'a biyar ga watan Isfand shekara ta dbu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ta fitar da wani bayani na yin Allah wadai da hare haren ta'addancin baya bayan nan da aka kai wa garuruwa daban daban a Iraki a ranar alhamis hudu ga watan na Isfand. A hare haren ta'addanci na ranar ta alhamis hudu ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya mutane da dama ne suka rasa rayukansu yayin da wasu kimanin dari hudu suka jikkata kuma wannan hari ne da babu wani mai hankali da tunani da tausayi da zai amince das hi. Wannan harin ta'addanci wani mataki ne na kawo Baraka da tashe tashen hankali da rashin tsaro a tsakanin al'ummomi da kabilu da mabiya addinai daban daban a wannan kasa ta Iraki kuma da yardarm Allah makiya musulmi da addinin musulunci ba za su taba cimma burinsu ba . gwamnatoci da hukumomi na yankin da na kasa da kasa da kungiyoyi daban daban na duniya suka yi ta yin Allah wadai da wadannan hare haren ta'addanci kan fararen hula da bas u san hawa balantana sabka day a hada yara da kananan yaro kuma irin wadannan hare hare da ake kai wa a cikin kasashen musulmi wani makirci ne na wargaza hadin kan musulmi domin makiya su cimma burin abin da suke ke son cimma a kasashen musulmi amma da yardarm Allah ba za su taba cimma burinsu ba.
959563