Bangaren siyasa da zamantakewa; a karo na biyu ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriayr musulunci a kasashen Afrika tare da shugaban hukumar kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci a kasashe daban daban na duniya ya tafi kasar Tanzaniya domin bude ofishin hukumar.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a karo na biyu ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriayr musulunci a kasashen Afrika tare da shugaban hukumar kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci a kasashe daban daban na duniya ya tafi kasar Tanzaniya domin bude ofishin hukumar. Muhammad Bakir Khuramshahar shugaban hukumar kula da yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a ranar hudu ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya bayyana manufa da burin kara fadada dangantaka ta al'adu da addini a tsakanin kasashen nahiyar Afrika da kuma takwararsu ta jamhuriyar musulunci ta Iran. Har ila yau ya kara da cewa wannan wani babban mataki ne na inganta wannan fanni da kuma zai taimaka matuka gaya ta fuskoki daban daban musamman idan kuwa ya yunkuro da kuma ya yi aiki da nauyin day a rataya kansa . idan aka yi la'akari da al'ummomin biyu za a ga cewa sun hada abubuwa da dama masu amfani da za su taimaka masu ta bangarori da dama da samar da fahimtar juna da hadin kai.
960375