IQNA

Fadakar Musulmi Wata Shinfida Ce Ta Kawar Da Gwamnatin Mamaya

Bangaren al'adu da fasaha: Ahmad Alkahlawi ya jaddada cewa: wannan sauye sauye da canje canje na fadakar musulmi a kasashen larabawa da na musulmi wata babbar shinfida ta kaiwa ga nasarar kawar da gwamnatin mamaye da wuce gonad a iri ta yahudawan sahayoniya da cewa: ta hanayr tunani ,rubuce-rubuce da fasaha za mu kare al'ummar palasdinu da ake zalunta.




Kamfannin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani ami girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Ahmad Alkahlawi ya jaddada cewa: wannan sauye sauye da canje canje na fadakar musulmi a kasashen larabawa da na musulmi wata babbar shinfida ta kaiwa ga nasarar kawar da gwamnatin mamaye da wuce gonad a iri ta yahudawan sahayoniya da cewa: ta hanayr tunani ,rubuce-rubuce da fasaha za mu kare al'ummar palasdinu da ake zalunta.A kasar Tunusiya ce ofishin da ke kula da harkokin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a ketare ya shirya wata kasuwar baje koli ta fasaha da gwagwarmaya a kasar Tunusiya tare da hadin guiwar kungiyoyin taimakawa palasdinu. Da dama daga cikin wadanda suka halarci wannan kasuwar baje kolin sun bayyana cewa irin sauye-sauyen da ake samu da canje canje a wanann yanki ko shakka babu wata alama ce da shinfida kai wag a cin nasarar kawar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a doran kasa da kawo karshen zaluncin da ake nunawa al'ummar palsdinu yau sama da shekaru sama da hamsin ba tare da gwamnatoci na yanki da na kasa da ksa da hukumomi na yanki da na kasa da kasa sun yi wani abun da zai kawo karshen wannan zalunci a fili karara.

961181