IQNA

Gina Mahanga Kan Shari’a Shi Ne Matakin Farko Na Bin Sahihin Tafarki Na Irfani

Bangaren fikira, gina mahanga kan tafarki na sharia’ da bin sahihan nassosinta da hukuncinta shi ne mataki na farko na bn sahihin tafarkin irfani, domin bin abin da ya sabawa shari’ar ubangiji ba shi da wata dangataka da tafarkin irfani na gaskiya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hoj. Eslam Dr. Muhammad Taqi Fali malamin jami’a da kuma cibiyar ilimi da bincike kan ilmomin addinin muslunci ta Hauza ya bayyana cewa gina mahanga kan tafarki na sharia’ da bin sahihan nassosinta da hukuncinta shi ne mataki na farko na bn sahihin tafarkin irfani, domin bin abin da ya sabawa shari’ar ubangiji ba shi da wata dangataka da tafarkin irfani na gaskiya kamar yadda wasu suke rayawa.
Bayan da muka kawo wasu abubuwa game da ranaku da daruruwa, yana da kyau mu yi ishara game da mahangar Ahlul sunnah, wanda zamu iya takatata a cikin wanan babi, to yanzu a gaban mu akwai abubuwa muhimmai masu yawa:
Na farko: lallai ranaku masu daraja sun kebanta da raya su da ibadar da abin da dare ya kebanta dashi na ibada na kebancewa ga Allah wajen ganawa da shi da yin addu'oi da yin bauta gare shi madaukakin sarki, kuma abin da yake da gayan muhimmanci a ciki shi ne kula da tsarkin ruhu da yake kunshe cikin yin wanka.
Na biyu: lallai wadannan ranaku masu daraja kamar ranakun idi suke sun kebanta da batun yin tsafta da kawa wato ado, don haka ma aka jaddada game da yin wanka da fesa turare da kuma sanya tufafi masu kyau, haka kuma ta kebanta da yin ayyukan da suka shafi zaman tekwar jama'a ta yyada salloli a cikinsu tana dacewa da irin yanayin ranar, kamar yadda yake a ranar Juma'a da idin karamr sallah da babba, hakan nan ya jaddada game da muhimmacin ziyarar yan uwa da abokan arziki da kyautatawa a cikinsa, da dai sauran abubuwan da suka shafi zamantakewar al’umma .
Na uku: bayani game da wila'a da nuna soyayya ga ahlul baiti (as) da kuma samun alaka dasu tare da yin koyi dasu tare da girmama ayyukansu da kuma barranta ga makiyan su, aikata irin wadanan ayyuka yana nuna hakikanin zahirin abubuwan da dararen da sauran ranaku masu daraja suka kebanta da shi. Wannan na nuna cewar komai ya bayyana afili idan aka yi la'akari da irin jaddadawar da aka yi, game da Ziyarar Imam Hussain da Imam Ali (as) da ake yi a cikin su, haka ma ya waita yin salati ga manzo da iyalan gidan sa kai dama danganta wadannan ranaku da abin da ya dace da su.
Na Hudu: lallai yin ibada da ta shafi azumi tana da wasu abubuwa na musamman a cikin wadannan ranaku masu daraja, a cikin ranakun idin karamar sallah da babba an haramta yin wannan ibada a cikinsu domin abin da ake bukata a cikinsu shi ne lizimtar kau da kai ga wadannan ayyuka, sai dai mustahabi mai tsanani ne a cikin wasu ranaku kamar a ranaku hudu sai dai babu wani jaddadawa da ya zo game da mustahabancin yin azumi a ranar Juma'a, sai dai a cikin wani yanayi na musamman, misali don neman biyan bukata ko kuma cika azumin ranar laraba da Alhamis.
Na biyar: Rabe-raben ranaku da darare bisa tsare-tsaren ibadodi a mafiyawan cin watannin shekara, kamar a watan Rajab, Sha'aban, Ramadan, Shawwal, Zulki'ida, da kuma zul hijja, da Rabiul Awwal, to idan muka kara wasu bukukuwan na musamman na ahlul bati (as) akan su wadannan ranaku za su kasance sun cika cif a tsarin shekara dukkanta.
NA Shida: Mafi yawancin fadada bayani da ake yi a kan wadannan ranaku da darare da kuma sabanin da ake samu a cikin su, yana zuwa ne kawai domin a ciki wadannan gurabe da aka bari dake wakiltan wannan nazari. Za a ga an sanya su ne bisa tsari da Ahlul baiti suka kafa domin tarbiyantar da ruhin mutane da halaye nagargaru, da kuma gina zuciya da karfin iko da kuma kamalar ruhi da warkar da cututtukan rai da ruhu.
Na Bakwai: lallai abin la'akari game da ranaku da darare shi ne dukkan tsarin jadawalinsu, da ayyukan da ake yi a cikinsu suna zama tamkar cigaba ne har zuwa ranakun juma'a, da idodin karama da babbar sallah, da ma daren Juma'a da daren lailatul kadr, ta yadda ibadodi da ayyuka za su tabbata a cikin wadannan darare da ranaku, wato tushen da dukkan ayyuka da ibadodi a wasu dararen da ranaku suka samo asali, wanda hakan yasa muka gane cewa lallai abin da ya zo daga ahlul baiti (as) na abin da ya shafi wadannan darare da ranaku, imma ya kasance daga iliminsu yalwatacce ne game da hukumce-hukumcen shari'a, ko kuma yana bayyana hakikanin asalin mahangar shari'a da abubuwan da ta ginu a kai, ta yadda za a iya ciro dukkan wadannan bayanai daga gare ta bisa asasin abinda aka rawaito daga Imam Ali (as) na daga maganganunsa cewa Manzon Allah ya karantar da ni babi dubu na ilimi, kuma kowanne babi yana bude min babi dubu na ilimi.
910887