Bangaren fikira, marigayi Imam khomeini daya ne daga cikin fitattun malaman addini wadanda suka hada dukaknin bangarori na ilimi a cikin rayuwarsu da hakan ya hada ilmomi na fikihu da dukaknin rassansa da kuma bangare irfani a gefe guda, kamar yadda rubutunsa da zantukansa suka tabbatar da hakan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hoj. Eslam Dr. Muhammad Taqi Fali malamin jami’a da kuma cibiyar ilimi da bincike kan ilmomin addinin muslunci ta Hauza ya bayyana cewa, marigayi Imam khomeini daya ne daga cikin fitattun malaman addini wadanda suka hada dukaknin bangarori na ilimi a cikin rayuwarsu da hakan ya hada ilmomi na fikihu da dukaknin rassansa da kuma bangare irfani a gefe guda.
Yana daga cikin ababen girmamawa na musulunci a wajen bayin Allah na gargaru wato masallaci da kuma wurare masu tsarki, da kuma ma yadda kebanta tare da ba su muhimmanci na musamman a mahangar ahlul baiti (as) kuma sukan banbanta da zurfinsu da yalwansa, da kuma abubuwan da suka kunsa wannan a bangaren ranaku masu daraja kenan wadanda muka yi bayani a kansu a baya.
Batun wurare masu tsarki wani batu ne da dukkan muslumi suka hadu a kai, haka ma dukkan addinai da aka saukar daga sama suma sun yi ikirari da su. Sanannen abin girmamawa a wajen musulmai gaba daya shine (massalaci) wanda yake wuri ne na ibada ga musulamai. hakika an yi ishara a kan shi a wurare daban-daban a cikin alkur'ai mai girma, fadarsa madaukakin sarki: "Abin sani kwai mai raya masallatan Allah shi ne wanda ya yi Imani da Allah da ranar lahira, kuma ya tsayar da sallah kuma ya bayar da zakka kuma bai ji tsoron kowa sai Allah, to akwai tsammanin wadannan su kasance daga shiryayyu." Haka kuma fadarsa madaukakin sarki: "kuma ku tsaida fuskokinku a wurin kowanne masallaci, kuma ku roke shi kuna masu tsarkake addini gare shi, kamar yadda ya fara hallitar ku kuke komawa, har ila yau a fadarsa madaukakin sarki: "dukkan wuraren sujjada na Allah ne kada ku kira wani tare da Allah (3) haka ma sun zo a cikin wasu ayoyi daban-daban.
Kuma (Musallah) ga yahudawa ko kuma ga Sa'ibawa kamar yadda ya zo a cikin fadarsa madaukakin sarki game da batun wadannan sunaye "kuma ba don tunkudewar Allah ga mutane ba sashinsu da sashi hakika da an rusa Sauma'oin (Ruhbaniyawa) da majami'oin Nasara da gidajen ibadar yahudawa da massalatai wadanda ake ambatar Allah a cikin su da yawa, kuma lallai hakika Allah yana taimakon wanda ya taimake shi lallai hakika Allah ne mai karfi kuma mabuwayi."
Hakika masallaci yana da muhimmiyar rawa da yake takawa a cikin shari'a muslunci ba wai kawai ya kebanata da yin ibada ne kawai a cikinsa ba, baya ga wannan ma a bangare guda akwai rawar da yake takawa da ya shafi wayar da kai da karantarwa, da kuma bitar harkokin siyasa da karfafa ruhin jama'a, kamar yadda ake amfani da shi a farko-farkon bayyanar musulunci misali wajen tafiyar da al‘amuran mulki da alkalanci da kuma shiga tsakanin masu rigima, wanda hakan yasa masallaci ya zama cibiyar ibada da wayar da kai da siyasa da kuma koyar da ya abin da ya shafi zamantakewar jama'a, kuma yana cigaba da gudanar da ayyukan sa tsakanin al’ummar musulmi tare da kiyaye tsarkinsa da kuma girmam war da ake yi masa.
Don haka za mu ga cewa dukkan yawan nassoshin da suka zo daga iyalan gidan manzo (saww) suna yin bayani ne game da hukumce hukumcen masallaci da laddubansa da sha'anoninsa da kuma yadda mutum zai yi mu’amala da shi cikin girmamawa, da tsarkake shi da kuma kula da ginin sa da yin Ibada a cikinsa da kuma irin ladar dake tattare da kai kawo a cikin sa tare da yin salla da I'itikafi da ma zama a cikinsa.
910885