IQNA

Taron Karawa Juna Sani Kan Yadda Musulunci Ke Yakar Ayyukan Assha

Bangaren kasa da kasa: a taron karshe na jerun tarurruka a sheakara ta dubu biyu da goma sha daya miladiya a Talamsan babban birnin al'adu na duniyar musulmi a shekara ta dubu biyu da goma sha daya da za a fara gudanarwa a ranar sha shida ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya an bashi taken addinin musulunci da kuma yadda yake yakar duk wani aiki na ashha da nuna mugunta.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a taron karshe na jerun tarurruka a sheakara ta dubu biyu da goma sha daya miladiya a Talamsan babban birnin al'adu na duniyar musulmi a shekara ta dubu biyu da goma sha daya da za a fara gudanarwa a ranar sha shida ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya an bashi taken addinin musulunci da kuma yadda yake yakar duk wani aiki na ashha da nuna mugunta.An nakalto daga jaridar Alkhabar da ake bugawa a kasar aljeriya cewa wannan taron ma'aikatar da ke kula da harkokin addinin musulunci a kasar ta Aljeriya ta shirya kuma za a ci gaba da gudanar da wannan taro har zuwa ranar sha takwas ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya. Har ila yau a lokacin gudanar da wannan taro malamai dam asana da wakilan gwamnati za su yi nazari kan abubuwan da ke haddasa aikata ayyukan assha da mugunta a fadin duniya da kuma tunanin hanyoyin rage yaduwar ayyukan assha da ma magance su.
963048