Bangaren harkokin kur'ani: an gudanar da taron karawa juna sani da bincike a jami'ar musulunci ta garin Aligar a lardin Utarpardash na kasar Indiya a dakin taro na Muhammad Habib na wanan jami'ar kuma taron ya kumshi rawar da kur'ani ke takawa wajan ciyar da ilimi da ci gaban fasaha da koyarwa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; an gudanar da taron karawa juna sani da bincike a jami'ar musulunci ta garin Aligar a lardin Utarpardash na kasar Indiya a dakin taro na Muhammad Habib na wanan jami'ar kuma taron ya kumshi rawar da kur'ani ke takawa wajan ciyar da ilimi da ci gaban fasaha da koyarwa.Mahalarta taron day a hada malamai da kuma masana da malaman tarihi sun afara taron ne tun ranar shida da watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya zuwa takwas ga watan na isfand inda kowa ya kawo bayani da bincikensa kan wannan lamari na irin rawar da kur'ani ke takawa ta fuskar yada ilimi da ci gaban fasaha kuma su kansu malaman jami'a sun bayar da tasu gudunmuwar.
962517