IQNA

Fara Taron Nemo Hanayr Yakar Gina Matsugunnan Yahudawa A Kudus

Bangaren kasa da kasa; a jiya ne sha hudu ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Oman fadar mulkin kasar Jodan karkashin kulawa da daukan nauyin hukumar kula da al'adu da ilimi Esesko ta kungiyar hadin kan kasashen musulmi aka fara gudanar da wani taro na neman hanyoyi da salon yakar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a siyasarta ta ci gaba da gina matsugunnan yahudawa yan share guri zauna a yankunan kudus mai tsarki.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a jiya ne sha hudu ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Oman fadar mulkin kasar Jodan karkashin kulawa da daukan nauyin hukumar kula da al'adu da ilimi Esesko ta kungiyar hadin kan kasashen musulmi aka fara gudanar da wani taro na neman hanyoyi da salon yakar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila a siyasarta ta ci gaba da gina matsugunnan yahudawa yan share guri zauna a yankunan kudus mai tsarki.An nakalto daga jaridar Alyaum Sabi'I da ake bugawa a kasar Masar cewa a wannan zama da taron shi ne irinsa na biyar da hukumar Asesko ta gudanar da irinsa tare da hadin guiwar komitin kula da ilimi da al'adu da abubuwa na tarihin na Palsdinu da ked a matsugunni a kasar Jodan. Kuma wannan taron a yau ne za a kawo karshen tare da fitar da jawabin kawo karshen wannan taro da kuma yin bayani dalla dalla kan hanyoyi da salon fuskantar bakar siyasar gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ta ci gaba da gune gunan matsugunnan yahudawa yan share guri zauna a yankin Kudus mai tsarki duk da kiraye kirayen da hukumomi da kungiyoyi na kasa da kasa ke yi wa Haramtacciyar kasar ta Isra'ila kan ta dakatar da wannan bakar siyasa tat a.
965146