IQNA

Samar Da Dakin Mai Dumin Na Musamman Ga Mahajjata

Bangaren kiwon lafiya: shugaban cibiyar kula da likitoci masu kula da mahajjata da guraren ziyara na HilalunAhmar ya bada labarin samar da wani daki na musamman dauke da abubuwan dumama daki ga maniyata aikin Hajja da kuma suke fama da rashin lafiya kuma za a ajiye su a asibitoci da ccibiyoyin ajiyar magunguna domin amfani da su idan bukatar hakan ta taso.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: shugaban cibiyar kula da likitoci masu kula da mahajjata da guraren ziyara na HilalunAhmar ya bada labarin samar da wani daki na musamman dauke da abubuwan dumama daki ga maniyata aikin Hajja da kuma suke fama da rashin lafiya kuma za a ajiye su a asibitoci da ccibiyoyin ajiyar magunguna domin amfani da su idan bukatar hakan ta taso. A wani taron manema labarai ya yi bayani kan cewa ganin lokacin zabin na kuratowa kuma ana fuskantar wannan matasala da zafi a kasar Saudiya musamman ga masu aikin hajji da ziyartar dakin Allah mai girma ya sa suka yi tanadin dakuma masu bada sanyi da sanyaya dakin ga masu fama da rashin lafiyar tsananin zafi. Tuni aka bayyana gamsuwa da wannan shiri da suka ce zai taimakawa masu ziyara a kasar Saudiya.


965197