Bangaren siyasa da zamantakewa; a yau takwas ga watan Maris shekara ta dubu biyu da goma sha biyu wanda ya yi daidai da ranar sha takwas ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da goma sha biyu hijira shamsiya za a fara gudanar da wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu da aka bawa taken hakkokin bil adama da mata a kasar Indiya da karamar jami'a mai kula da ilimi na zamantakewa da bincike a jami'ar Maulana Azad a garin Haidar Abad na Indiyan ta shirya.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a yau takwas ga watan Maris shekara ta dubu biyu da goma sha biyu wanda ya yi daidai da ranar sha takwas ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da goma sha biyu hijira shamsiya za a fara gudanar da wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu da aka bawa taken hakkokin bil adama da mata a kasar Indiya da karamar jami'a mai kula da ilimi na zamantakewa da bincike a jami'ar Maulana Azad a garin Haidar Abad na Indiyan ta shirya.A lokacin bude wannan taron akwai Hamid Na'im daya daga cikin yan jami'ar Kashmir da zai gabatar da jawabi a matsayinsa na bakon musamman a gurin wannan taro . Har ila yau a gurin wannan taron za a samu halartar malaman jami'a manya na indiya da za su fito daga jami'o'I daban-daban na kasar da kuma wasunsu za su gabatar da jawabi kan lamarin da za a tattauna kansa a wannan taron.
966844