Bangaren kasa da kasa; babban masallaci a birnin Paris na kasar Faransa ya bayyana cewa; nan bad a jimawa ba za a kafa wani komiti na musamman kuma na addini da zai gudanar da bincike kan lamarin day a shafi yankan musulunci yankan halal da kuma dokokin addinin musulunci kan wannan lamari.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; babban masallaci a birnin Paris na kasar Faransa ya bayyana cewa; nan bad a jimawa ba za a kafa wani komiti na musamman kuma na addini da zai gudanar da bincike kan lamarin day a shafi yankan musulunci yankan halal da kuma dokokin addinin musulunci kan wannan lamari.An jiyo daga Europe 1 cewa: dalili Bubakar shugaban babban masallacin na birnin Paris da kuma shugaban cibiyar koyarwa ta masallacin na cewa: domin fayyace lamarin za a kafa wani komiti na musamman da zai yi nazari da bincike kan yankan musulunci kuma wannan komiti na addini zai kumshi malamai dam asana harkokin addini da hukumce-hukumce.Ya kara da cewa; mambobin wannan komitin za su yi tarurruka na kwararru da bincike da tattaunawa kan hukumce hukumcen addinin musulunci da suak shafi yankan musulunci kuma shin hukumci na fikhu da yanayi sun bada dammar canja salon yanka ko a'a.Wannan lamari ya biyo bayan yadda maganar yankan musulunci da na yahudawa ya zama lamarin yin Magana kansa a tsakanin yan takarar neman shugabancin kasar Faransa hart a kai na baya bayan nan shi ne firaminitan Faransa day a ce salon yanka na musulmi ba irin n azamani ne ba.
968238