Bangaren al'adu da fasaha; an nuna littalin Al'imam Khomeini Al'asala wattajadid da hujjatul islam wal muslim na'ima Kasim mukaddashin babban sakataren kungiyar Hizbullahi a kasar labanon ya rubuta.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an nuna littalin Al'imam Khomeini Al'asala wattajadid da hujjatul islam wal muslim na'ima Kasim mukaddashin babban sakataren kungiyar Hizbullahi a kasar labanon ya rubuta. Wanna littafi ya kumshi bayanin tunani da zanari da hagen nesa da siyasar imam Khomeini ® kuma an yi buki na musamman a birnin Beirut a ofishin da ke kula da yada al'adun jamhuriyar musuluncin ta Iran a kasar Labanon wajan nuna wannan littafi a ranar sha shidda ga watan isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da ti'sin hijira shamsiya kuma marubucin wannan littafi ya bayyana cewa shi ne ya gay a dace ya rubuta wannan littafi domin ko ba komi Imam Khomeini makaranta c eta tunani da nazari da aiki a musulunce.
968859