Bangaren kasa da kasa; bayan yin kuri da nema haka babu kasawa na tsawon lokaci mai tsawo a karon farko an amince da kafa wata cibiyar ta tattaunawa da fahimtar juna a tsakanin musulmin kasar Italiya da zummar kara kusanci a tsakanin masallata da masu kula da masallatai a wannan kasar da kuma uwa uba kare hakkin musulmi a wannan kasa.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: bayan yin kuri da nema haka babu kasawa na tsawon lokaci mai tsawo a karon farko an amince da kafa wata cibiyar ta tattaunawa da fahimtar juna a tsakanin musulmin kasar Italiya da zummar kara kusanci a tsakanin masallata da masu kula da masallatai a wannan kasar da kuma uwa uba kare hakkin musulmi a wannan kasa.An jiyo daga majiyar labarai ta Islam Today cewa; tun shekara ta dubu biyu da tara miladiya ne taka bada shawarar kafa wannan dakin shawara na musulmi kuma har zuwa wannan lokaci cibiyar kula da al'adun musulunci a Italiya da kuma ofishin babban masalacin kasar sun yi ta kokari da bin diddigin wannan lamari har zuwa wannan lokaci kwacam aka amince da kafa wannan dakin shawara na musulmi kuma bayan lura da bin diddigin lamura da suka shafi kare hakkin musulmi a wannan kasa kuma za su rika kalubalantar duk wani lamari na takurawa musulmi da cin zarafinsu a wannan kasa tare da bawa musulmin kasar ta italiya ynaci da damar yin ibadodinsu.
974778