IQNA

HKI Ta Hana Musulmi Shiga Hubbarin Ibrahim

Bangaren kasa da kasa: sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila a ranar ashirin ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a garin Khalil ta hanyar fakewa da idin kirsitoci da ke gudanar da bukin tunawa da ranar da bani isra'ila suka fice daga Masar sun hana musulmi shiga hubbarin Ibrahim.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kuma da harkokin kur'ani mai girmna a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila a ranar ashirin ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a garin Khalil ta hanyar fakewa da idin kirsitoci da ke gudanar da bukin tunawa da ranar da bani isra'ila suka fice daga Masar sun hana musulmi shiga hubbarin Ibrahim. Har zuwa wannan rana ta yau ashirin da daya ga watan na farvardin wannan guri na ci gaba da kasancewa a rufe ga musulmi wato ana hana musulmi shiga wannan guri mai muhimmanci domin yin ziyara da ibadodinsu . Tuni kungiyoyi da shugabannin addini suka fara bayyana ra'ayin su da sukar wannan mataki na ganganci da takalar fada da nuna wariya kan musulmi da gwamnati ta dauka na umurtar sojojinta na su hana musulmi shiga wannan guri musamman a daidaid wannan lokaci.
981713