IQNA

Al'ummar Najeriya Na Adawa Da Hana Sanya Hijabi A Makarantun Kasar

Bangaren kasa da kasa; musulmi a birninnlagos na kasar Nigeria da kuma kungiyoyin loyoyi na musulmi a wannan kasar sun yi niya a ci gaba da nuna adawa da zanga zangar da suke yi kan matakin hana yan mata sanya hijabi a makarantun gwamnati su shigar da karar gwamnatin kasar a gaban kuliya domin kare masu hakkokinsu.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: musulmi a birninnlagos na kasar Nigeria da kuma kungiyoyin loyoyi na musulmi a wannan kasar sun yi niya a ci gaba da nuna adawa da zanga zangar da suke yi kan matakin hana yan mata sanya hijabi a makarantun gwamnati su shigar da karar gwamnatin kasar a gaban kuliya domin kare masu hakkokinsu.An nakalto daga majiyar labarai ta Muslim village cewa; karkshin wannan shirin na gwamnatin tarayyar Nigeria na kokarin hana yan mata sanya hijabi a makarantu da cewa dole lokacin da suke kokarin shiga makaranta su fidda hijabi dad an kwalin da ke kansu sai dai daftarin doka na fuskantar gagaramin suka da kalubale daga musulmi a fadin kasar musamman ma musulmi da ke birnin Lagos babban birnin kasuwancin kasar kuma hatta lauyoyi na musulmi da uwayen yara yan makaranta musulmi day an matan da wannan daftarin doka ke neman shafarsu sun gudanar da gagaramar zanga-zangar yin Allah wadai da yin jifa da wannan mataki na gwamnatin tarayyar Nigeria. Tuni kungiyoyi da manyan malamai dam asana kasar suka fara bayyana cewa wannan wata doka c eta nuna wariya kan musulmi kuma dole abi dokokin da hanyar tattaunawa domin yin watsi da wannan doka kuma idan bah aka ba za su bi hanyar da suka gat a dace su bi domin kalubalantyar wannan doka. Kasar Nigeria dai tana da mutane sama da miliyon dari da arba'in kuma kasha satin daga cikinsu musulmi ne yayin da kuma kasha arba'in kiristoci ne.

984522