IQNA

Hadin Guiwar Yan Azhar Na Adawa Da Takarar na Kusa Da Mubarak

Bangaren kasa da kasa: hadin guiwar masu yada addini na jami'ar azhar sun fitar da wata sanarwa da acikinta suka bayyana adawarsu a fili karara da yadda wasu na hannun dama kuma na kusa da tsohon shugaban kasar kasar dan kama karya Husuni Mubarak kuma masu fada a ji a gwamnatinsa suka ajiya neman a bas u damar tsayawa takarar neman shugabancin wannan kasa.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: hadin guiwar masu yada addini na jami'ar azhar sun fitar da wata sanarwa da acikinta suka bayyana adawarsu a fili karara da yadda wasu na hannun dama kuma na kusa da tsohon shugaban kasar kasar dan kama karya Husuni Mubarak kuma masu fada a ji a gwamnatinsa suka ajiya neman a bas u damar tsayawa takarar neman shugabancin wannan kasa.Sheik Khalf Mas'ud mai kula da bangaren hulda da jama na jaridar Ahram ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan Iran cewa da dama daga cikin malamai da masu yada addini a wannan babbar jami'a da ta yi suna a duniyar musulmi kuma mai daden tarihi a harkar yada addini da ilimi a duniya sun bayyana adawa da takaicinsu da yadda wasu na hannun dama kuma na kulkusa da suka taka rawa a gwamnatin dan kama karya Husni Mubarak suka nemi a bas u damar tsawa a zaben shugabancin kasar da za a gudanar da hakan ke nuni da yadda ake neman a maida hannun agogo baya da zama yunkuri juyin da al'ummar kasar masar suka yi ya zama tamkar ihunka banza ne . To saidai gagaramar adawa da kiyayyar da al'ummar kasar ke nunawa ya sa lamarin na neman ya canja kuma da wuya hukumar da ke tamtamce yan takara ta bar su su tsaya wannan takarar kuma idan kuwa aka bar su ko shakka babu za a samin matsin lamba daga al'ummar kasar a dandalin tahrir.

985799