IQNA

Wakilan Hamas Da Jihadul Islami Sun Halarci Komitin Tsaro Na Majalisar Iran

Bangaren siyasa :a zaman da komitin tsaro da kuma da siyasar waje a majalisar shawara ta musulunci a ranar ashirin da tara ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya an samu halartar Khalid Kudumi wakilin kungiyar gwagwarmaya ta Hamasa da kuma Nasir Abu Sharif wakilin kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul Islami kuma an gayyace su ne a dadlin tunanawa ranar yan gidan yarin Palasdinu.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; a zaman da komitin tsaro da kuma da siyasar waje a majalisar shawara ta musulunci a ranar ashirin da tara ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya an samu halartar Khalid Kudumi wakilin kungiyar gwagwarmaya ta Hamasa da kuma Nasir Abu Sharif wakilin kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul Islami kuma an gayyace su ne a dadlin tunanawa ranar yan gidan yarin Palasdinu. Tun farkon fara zaman wannan komitin Khalid Kadumi ya gabatar da wajabin yin godiya da girmamawa ga al'ummar Iran da kuma mahukumtan jamhuriyar musulunci ta Iran kan yadda suka dauki niya da matsaya ta kare da goyan bayan al'ummar Palasdinu a daidai lokacin da ake yi masu taron dangi na take masu hakkoki da yancinsu da kuma goyan bayan da suka nunawa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas da cewa; yana fatar Iran da sauran kasashe za su ci gaba da yin Allah wadai da harindabbanci da rashin tausayi da ake nunawa al'ummar palasdinu kuma yana fatar za a tilasta ma Haramtacciyar kasar Isra'ila bi da mutunta dokokin kasa da aksa.Kuam ya yi kira da babbar murya da mu'assishi da hukumomi na kasa da aksa da cibiyoyi das u yi dubi da halin da al'ummar palasdinu ke ciki da kuma yunkurowa na ganin an kawo karshen killacewar da aka yi wa al'ummar yankin zirin gaza. A cikin jawabin nasa yayi tsokaci da bayani kan halin kunci da takurawa da al'ummar Palasdinu ke ciki a gidajan yarin Haramtacciyar kasar Isra'ila da ake tsare das u da kuma yadda ake takura masu da hana su walwala kamar sauran al'ummomi na duniya.

988403