IQNA

Ci Gaba Da Taron Karawa Juna Sani Kan Tarihin Fatimatu Zahra (AS)

Bangaren ilimi da nazari" a kasar Indiya malamai dam asana da kuma dalibai da suaran musulmin wannan kasa na ci gaba da gudanar da tarurruka iri iri kuma masu yawa kan tarihin Fatimatul Zahra (AS) diyar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka har ila yau a bangare guda akwai falolinta da kywawan halayanta da kuma binciken hudubarta kan fadak.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a kasar Indiya malamai dam asana da kuma dalibai da suaran musulmin wannan kasa na ci gaba da gudanar da tarurruka iri iri kuma masu yawa kan tarihin Fatimatul Zahra (AS) diyar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka har ila yau a bangare guda akwai falolinta da kywawan halayanta da kuma binciken hudubarta kan fadak. Manyan malamai da manazarta da kuma wakilan gwamnati da na yankin suka halarci irin wadannan tarurruka na karawa juna sani da kuma bincike kan tarihin fatimatul Zahra (AS) kuma da dama daga cikin wadannan suka yi sa'ar halartar irin wannan taro sun gamsu da farin cikin yadda aka yi masu bayanai masu gamsarwa da kuma kayatarwa kan halaye da falollin wannan baiwar Allah wadda ta sadaukar da raid a rayuwarta wajan ciyar da addinin musulunci da kuma ta yi gwagwarmaya da sadaukar jininta wajan yada addinin musulunci .Kuma kow ya shaida rawar da ta taka a wannan fanni kamar yadad ma'aifinta manzon rahama Muhammadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa ya shaida mana kuma sauran sahabban ma'aikin Allah sun shaida haka saidai kawai mu yi fatar Allah ya daura mu a kan damshinta amin summa amin.
994149