Bangaren al’adu da fasaha, gwagwarmayar musulunci ta koyar da haramtacciyar kasar Isra’ila babban darasi wanda ba za ta tabata manta da shi ba a cikin tarihinta kuma hakan ya sanya yahudawan sahyuniya sake tunani kan cewa za a iya lallasa su a hannun kungiyoyin gwagwarmaya masu tsarkakakkiyar zuciya.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shain sadarwa na yanar gizo na babbar cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adu cewa, gwagwarmayar musulunci ta koyar da haramtacciyar kasar Isra’ila babban darasi wanda ba za ta tabata manta da shi ba a cikin tarihinta kuma hakan ya sanya yahudawan sahyuniya sake tunani kan cewa za a iya lallasa su a hannun kungiyoyin gwagwarmaya masu tsarkakakkiyar zuciya.
Ko shakka babu a wannan zamani gwagwarmayar muslunci a kasar Lebanon ta hizbulla ta fitar da wani bayani da acikinsa take mayar da martani kan furucin sakataren majalisar dinkin duniya dangane da makaman kungiyar, inda bayanin ya ce hakkin lebanon ta mallaki makamai na gwagwarmaya domin mayar da martani kan wuce gonda irin yahudawan sahyuniya kan al’ummar Lebanon.
A cikin bayanin kungiyar ta yi kakkausar suka kan abin da ta kira rashin lamiri na mutumin da ake kira sakataren majalisar dinikin duniya, wanda ya kamata ya kare hakkokin mutane na kasashen duniya, amma maimakon hakan sai mayar da hankali wajen kare barnar da yahudawan sahyuniya suke aikatawa, tare da ba su kariya ta hanyar yin amfani da kujerarsa.
A lokutan baya ne Ban ki moon ya bayyan acewa, makaman da kungiyar gwagwarmayar muslunci ta hzibullah take mallaka barazana ce ga ita kanta kasar Lebanon.
998328