IQNA

Sabanin Mazhaba Kar Ya Kai Ga Canja Akalar Sauyin Da Ake Samu A Yankin

Bangaren kasa da kasa; sabani na mazhaba kar ya sa a canja akala da tushe manufa ta nema da kawo sauyi da canje canje da ake fuskanta a wannan yanki na gabas ta tsakiya musamman sauyi da fadakar musulmi a yanki domin idan ba a yi taka tsantsan ba makiya na iya amfanuwa da cimma mummunar manufarsu ta kawo sabani da ingiza wutar sabani a tsakanin musulmi su sa su manta da sha'afa da ainahin abin da suka sanya a gaba ko shakka babu su rungumi kabilanci da ta'assubanci na jahilci.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: sabani na mazhaba kar ya sa a canja akala da tushe manufa ta nema da kawo sauyi da canje canje da ake fuskanta a wannan yanki na gabas ta tsakiya musamman sauyi da fadakar musulmi a yanki domin idan ba a yi taka tsantsan ba makiya na iya amfanuwa da cimma mummunar manufarsu ta kawo sabani da ingiza wutar sabani a tsakanin musulmi su sa su manta da sha'afa da ainahin abin da suka sanya a gaba ko shakka babu su rungumi kabilanci da ta'assubanci na jahilci.A musalla na imam Khomeini ® da a halin yanzu ake gudanar da kasuwar baje kolin littafai ta kasa da kasa karo na ashirin da biyar a nan Tehran Ali Fiyad dan majalisar dokoki a kasar Labanaon a wani taron manema labarai day a gudanar a ranar sha bakwai ga watan Ordebehesht shekara ta dubu daya da da dari uku da tis'in hijira shamsiya a dakin taron na fadakarwar musulmi ya kara da bayyana cewa; abin da yake faruwa da fadakarwar musulmi a yau dol da hade dukan bangarori kama da siyasa zamanatake, bangarori da addini kuma a rika yin la'akarin da ra'ayin yawancin mutane da al'umma har ila yau a magance duk wani sabani na addini da mazhaba domin ta haka makiya ke son cimma manufarsu .
1001736