IQNA

Babu Wani Sharadi Da Saudiya Ta Shatawa Maniyata Hajji

Bangaren kiwon lafiya: mukaddashin hukumar da ke kula da ayyukan hajji a cibiyar da ke kula da likitoci na kungiya agaji ta Hilalul Ahmar ya bayyana cewa; babu wata kididdiga na Iraniyawan da suka kamu da wata cuta ta hana su yin aikin Hajji kuma babu wani rahoto kan haka kuma a dayan bangare ita kanta gwamnatin kasar Saudiya babu wani sharadi da ta kitta kan Iraniyawa das u yi aikin hajji ko zarginsu da kamuwa da wata cuta .



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci taIran ne ya watsa rahoton cewa: mukaddashin hukumar da ke kula da ayyukan hajji a cibiyar da ke kula da likitoci na kungiya agaji ta Hilalul Ahmar ya bayyana cewa; babu wata kididdiga na Iraniyawan da suka kamu da wata cuta ta hana su yin aikin Hajji kuma babu wani rahoto kan haka kuma a dayan bangare ita kanta gwamnatin kasar Saudiya babu wani sharadi da ta kitta kan Iraniyawa das u yi aikin hajji ko zarginsu da kamuwa da wata cuta .Walid Dandebar a wata tattaunawa ce da ta hada shi da kamfanin dillancin labarai da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya bayyana cewa:wannan labara da ake yadawa kan kamuwar Iraniyawa da wata cuta da hakan ya sa mahukumtan saudiya daukan matakin hana su zuwa wannan kasa domin gudanar da ayyukansu na sabke faralin aikin hajji kaai karya da wani lamari na kawo rudani da tsauro a cikin zukatan maniyata aikin hajji a bana daga jamhuriyar musulunci ta Iran.
1013305