Bangaren tunani da nazari: cibiyar da ke kula a yada labarai da suka shafi addini da kuma ta jiyo da ke ofishin da ke kula da harkokin addinin musulunci da lamuran da suka shafi musulmi a kasar Rasha ya bada labarin cewa a ranar shida ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya wato ranar asabar mai zuwa a birnin Masko za a gudanar da taron kasa da kasa na mata musulmi a wannan kasa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci taIran ne ya watsa rahoton cewa: cibiyar da ke kula a yada labarai da suka shafi addini da kuma ta jiyo da ke ofishin da ke kula da harkokin addinin musulunci da lamuran da suka shafi musulmi a kasar Rasha ya bada labarin cewa a ranar shida ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya wato ranar asabar mai zuwa a birnin Masko za a gudanar da taron kasa da kasa na mata musulmi a wannan kasa. Kungiyoyi da suke da dangantaka da ayyukan da suka shafi musulmi da addinin musulunci a wannan kasar ne za su halarci wannan taro kuma ana gayyatar duk wani musulmi da ke sha'awa wato duk mace da ked a sha'awar halartar wannan taro da za a tattauna lamura da suka shafi musulmi da zamantakewarsu kuma ana iya tuntubar bangaren da ke kula da wannan taro na kasa da kasa kan shafin Internet kamar haka: alshabah@wasatiya.ru ko lamba kamar haka:009067194363.
1012999