IQNA

Wakilan Kungiyoyin Masu ra'ayin Addini A Aljeriya Sun kauracewa Zaman majalisar na Farko

Bangaren kasa da kasa: wakilan kungiyoyi masu tsananin ra'ayin addinin musulunci a kasar Aljeriya a ranar shidda ga watan khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun kauracewa zaman majalisar karo na farko da hakan yake dangantaka da nuna adawarsu da rashin amincewarsu da sakamakon zaben yan majalisar dokoki a kasar .


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: wakilan kungiyoyi masu tsananin ra'ayin addinin musulunci a kasar Aljeriya a ranar shidda ga watan khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun kauracewa zaman majalisar karo na farko da hakan yake dangantaka da nuna adawarsu da rashin amincewarsu da sakamakon zaben yan majalisar dokoki a kasar .Su dai wakilan kungiyoyi masu tsananin ra'ayin addinin musulunci a kasar ta Aljeriya sun kauracewa zaman majalisar ne a ci gaba da nuna adawarsu da sakamakon zaben yan majalisar dokokin da aka gudanar day a nuna jam'iyu masu mulki a kasar ne suka lashe zaben da ke cike da rudani musamman a daidai wannan lokaci da ake fuskantar guguwar sauyi da canje canjen shugabannin da gwamnatoci a yankin gabas ta tsakiya da kuma yadda kungiyoyi da jam'iyu masu ra'ayin addini da samin karbuwa da nasara a tsakanin al'ummomin kasashen .To amma zaben da aka gudanar a kasar Aljeriya bah aka sakamakon ya nuna bad a hakan ya sa kungiyoyi masu tsananin ra'ayin addini ke dora ayar tambaya kan zaben da kuma sakamakon zaben da kuma yadda aka tafiyar da shi.

1017422