Bangaren kasa da kasa: komitin da ke kula da ofishin bugawa da watsa littafai a kasar Masar sun shirya wani zama na bincike da nazarin sabbin dokokin da suka shafi buga kur'ani mai girma da kuma yada shi kuma a wannan zaman bincike za a samu halartar Sheikhul azhar.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: komitin da ke kula da ofishin bugawa da watsa littafai a kasar Masar sun shirya wani zama na bincike da nazarin sabbin dokokin da suka shafi buga kur'ani mai girma da kuma yada shi kuma a wannan zaman bincike za a samu halartar Sheikhul azhar.
Wannan komitin da zai jagoranci wannan zaman bincike ya kumshi mutane uku daga ofishin da ke kula da bugawa da watsa littafai sai kuma mutane uku daga cikin kungiyar marubuta ta kasar ta Masar da kuma mutane uku wakilan guraren da ake buga littafan sai kuma sheikhul Azhar da za su yi nazari kan bugawa da watsa littaffai.
1016945