IQNA

An Buga Tare Da Yada Littafai Kan Fadakar Musulmi A Cikin harshen Kurwat

Bnagaren al’adu da fasaha, a daidai lokacin da ake guadanar da tarukan tunawa da marigayi Imam khomeni (RA) a kasashen musulmi da dama da mawasu kasashen turai an gabatar da wani littafi da aka buga dake bayani kan fadakar musulmi da kuma yadda wannan tunani ya samo asali daga kiran marigayi Imam Khomeni.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labaransa cewa, lokacin da ake guadanar da tarukan tunawa da marigayi Imam khomeni (RA) a kasashen musulmi da dama da mawasu kasashen turai an gabatar da wani littafi da aka buga dake bayani kan fadakar musulmi da kuma yadda wannan tunani ya samo asali daga kiran marigayi Imam Khomeni Allah ya kara masa yarda.
An raba wasu kwafofin kur’ani mai tsarki ga al’ummar palastinu mazauna yankin zirin Gaza wanda babbar cibiyar nan ta addini da ke kula da harkokin kur’ani a kasar Jordan ta kiyaye kur’ani ta taimaka wajen aiwatar da shirin kamar yadda ya gudana.
A bangare guda kuma Isma’il Haniyya pira ministan palastinu a yuankin Gaza ya bayyana cewa al’ummar palastinu suna gab da samun nasarar kwato masallacin Qods baki daya daga danniyar yahudawan sahyuniya wadanda suke hankoron rusa shi da kuma kawar da sauran dukaknin alamomi na musulmi baki daya.
Ya kuma byayana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi ga al’ummar kasar Tunisia a ziyarar da yake gudanarwa a wasui daga cikin kasashen yankin da suka hada Masar da kuma Suda gami da Turkiya, inda yake jadda matsayin kungiyar gwagwarmaya ta Hamas wajen ci gaba da yin gwagwarmaya domin samun ‘yancin al’ummar yankin na zirin Gaza.
Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, yankin gabas ta tsakiya ya zama wani wurin buga misali da gwagwarmayar neman ‘yanci da fita daga karshin mulkin zalunci da kama karya azzaluman shugabanninsu da suke azurta kansu da dukiyoyin da al’ummar kasar suke da su
1022393