IQNA

Musulmi A Kasar Iraki Sun Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Cibiyan Yan Shi'a

Bangaren kasa da kasa; musulmi a kasar Iraki da ya hada manyan yan shi'a da kuma yan sunna a wannan kasa sun fitar da wani bayani da a cikinsa suke yin Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai da bom kan cibiyar gudanar da harkokin addini nay an shi'a a akasar Iraki day a yi sanadiyar shahadar gomomin fararen hula da kuma jikkata wasu sama da dari da tis'in.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: musulmi a kasar Iraki da ya hada manyan yan shi'a da kuma yan sunna a wannan kasa sun fitar da wani bayani da a cikinsa suke yin Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai da bom kan cibiyar gudanar da harkokin addini nay an shi'a a akasar Iraki day a yi sanadiyar shahadar gomomin fararen hula da kuma jikkata wasu sama da dari da tis'in.Cikin wani bayani ne da kaukausar murya hadin guiwar musulmin Iraki day a hada yan shi'a day an sunna suka bayyana takaicinsu da kai wannan mummunan hari kan fararen hula dab a su san hawa balantana sabka ba kuma sun yi Allah wadai duk wani hari makamancin wannan tare da yin kira da babbar murya na musulmin kasar das u hada kansu na tunkarar duk wani makirci da ake kullawa al'ummar wannan kasa na haddasa fitina a tsakaninsu ta kowa ne hjali da yanayi da fatar Allah ya maidawa masu wannan mummunar niya aniyar .
1023012