IQNA

Ayyukan ta'addanci Ba Su Da Matsayi A Cikin Addinin Musulunci

Bangaren fikira da ilimi, wasu daga cikin malaman addinin muslunci dam asana a kasar India sun fitar da wani bayani na bai daya a cikin bayanin wani taro na karawa juna sani da suka gudanar da nufin wayar da kan al'ummomin duniya cewa ta'addanci bas hi ne musulunci ba kuma bas hi da wata alaka da muslunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gizo na bangaren yada labaransa na gabacin Asia, wasu daga cikin malaman addinin muslunci dam asana a kasar India sun fitar da wani bayani na bai daya a cikin bayanin wani taro na karawa juna sani da suka gudanar da nufin wayar da kan al'ummomin duniya cewa ta'addanci bas hi ne musulunci ba kuma bas hi da wata alaka da muslunci kamar yadda wasu suke dangantawa.
a lokacin da yake ganawa da shugaban majalisar shawar ta musulmin kasar Rasha, shugaban cibiyar Muhammad Baqir Khorramshad ya bayyana cewa addinin muslunci bai amince da tsatsauran ra'ayi na kin wasu sauran jama'a bad a hakan zai kai ga kafirta sauran musulmi da ma haslata jininsu ko haifar da rashin jituwa tsakanin mabiya addinin muslunci da wasu addinai na daba ta hanayar bayar da fatawoyi marassa kan gado da rashin ilimi ko sani makama.
Da dama daga cikin irin wadannan fatawoyin na haddasa fitina acikin al'ummar musulmi dai suna zuwa ne daga malman wahabiyawan saudiyya da suke kafirta sauran musulmi, wanda kuma da sannu al'ummar musulmi a duniya ta fara gano matsayin hakan tare da yi kanta kiyamullali.
1029875