IQNA

Komitin Dangantaka Ta Musulunci A Amerika Ya Bukaci Yin Bincike Kan Kai Wa Masallacin Karulina Hari

Bangaren kasa da kasa;komitin da ke kula da dangantaka da lamura da suka shafi musulmi a Amerika CAIR ya bukaci daya daga cikin shugabannin da ke kula da harkokin da suka shafi tsaro a lardin da kuma matakin kasa a Amerika day a gudanar da bincioke mai zurfi kan harin da aka kai wa masallacin Karolina da gano ko masu tsananin nuna adawa da musulunci ne suka kai wannan harin.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi Kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; komitin da ke kula da dangantaka da lamura da suka shafi musulmi a Amerika CAIR ya bukaci daya daga cikin shugabannin da ke kula da harkokin da suka shafi tsaro a lardin da kuma matakin kasa a Amerika day a gudanar da bincioke mai zurfi kan harin da aka kai wa masallacin Karolina da gano ko masu tsananin nuna adawa da musulunci ne suka kai wannan harin.A kasar Amerika kamar yawancin kasashen yammacin Turai ana fuskantar kai wa musulmi hari da kuma guraren ibadarsu da kuma hakan ke nuni da yadda ake kara samin masu adawa da musulmi a irin wadannan kasashe da kuma yadda harkokin da kara yin muni da kuma tabarbarewa ta fuskoki da dama da suka shafi tsaro da kuma zamantaewa da harkokin addini a irin wadannan kasashe.
1046680