IQNA

An Fara Gudanar Da Shirin KOyar Da Harshen Farisanci A kasar Sudan

Bangaren fasaha da al’adu, an fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan koyon harshen farisanci a kasar Sudan tare da halartar dalibai daga sassa na kasar da suke da matukar bukatuwa zuwa ga koyon harshen wanda ake Magana da shia ahukumance a wasu kasashen nahiyar asia da suka hada jamhuriyar muslunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habara cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka an fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan koyon harshen farisanci a kasar Sudan tare da halartar dalibai daga sassa na kasar da suke da matukar bukatuwa zuwa ga koyon harshen wanda ake Magana da shia ahukumance a wasu kasashen nahiyar asia da suka hada jamhuriyar muslunci ta Iran da kuma wasu kasashen an daban.
Har wala yau a kasar dai shugaba Umar Hasan Albashir ya isa kasar Habasha domin halattan zaman taron kungiyar tarayyar Afirika, inda ake sa ran zai tatatuna tare da takwaransa na kasar Sudan ta kudu.
Rahotonni sun bayyana cewar shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir ya isa birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha domin halattan zaman taron kungiyra tarayyar Afirika da za a fara gudanarwa a ranar lahadi mai zuwa.
Wakilin kasar Sudan a kungiyar tarayyar Afirika Abdurraham Sar-Khatam ya bayyana cewa shugaban kasar na Sudan zai gudanar da zaman tattaunawa da fira ministan kasar ta Habasha Males Zinawi dangane da shiga tsakani da kasar ta Habasha ke yi a rikicin kasar Sudan da makobciyarta Sudan ta Kudu.
A baya an shirya gudanar da zaman taron kungiyar ta tarayyar Afirika ne a kasar Malawi amma aka dage zuwa kasar Habasha sakamakon alwashin da gwamnatin Malawi ta yi na kame shugaban kasar Sudan Umar Hasan Albashir matukar ya shiga cikin kasarta domin mika shi ga kotun kasa da kasa da ke hukunta manyan laifuka a duniya da ke nemansa ruwa ajallo.
1052632