Bangaren fikira da ilimi, an bude wata makarantar koyar da falsafar Musulunci a birnin Jakarta fadar mulkin kasar Indonesia wadda za ta taka gagarumar rawa wajen kara yada mahangar malaman falsafar Musulunci domin warware matsaloli da suke tunkarar musulmi ta wannan fuska.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalato daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sucofindo cewa, a cikin wannan mako an bude wata makarantar koyar da falsafar Musulunci a birnin Jakarta fadar mulkin kasar Indonesia wadda za ta taka gagarumar rawa wajen kara yada mahangar malaman falsafar Musulunci domin warware matsaloli da suke tunkarar musulmi ta wannan fuska musamman a kasar wadda ta kasance ta farko wajen yawan musulmi a duniya.
Ko shakka babu kamar yadda ministan harkokin wajen HKI ya bayyana ne a ziyarar da ya kai Amurka a watan Fabrairun da ya wuce don neman goyon bayan Amurka kan amfani da karfi a kan Iran inda ya ce HKI tana da zabi daban-daban wajen fada da shirin nukiliyan na Iran. Duk da cewa batun kawo hari kan Iran ba abu ne mai sauki ba a gare su sakamakon abin da zai biyo bayan hakan, to amma ko shakka babu amfani da hanyar barazana da kisan gillan suna daga cikin hanyoyin da suka dauka don cimma bakar aniyarsu kan Iran. Akwai shaidu da yawan gaske da suke nuni da yadda kungiyar leken asirin ta yi amfani da wannan hanya ta kisan gilla don ciyar da manufar HKI gaban.
A 'yan watannin da suka gabata ma dai jaridar Sunday Telegraph ta Birtaniya ta buga wani labara da ke nuni da hannun kungiyar leken asirin HKI cikin kisan gillan da aka yi wa masanan na Iran cikin shekaru biyun da suka gabata. Ko shakka babu abubuwan da wadannan 'yan jarida suka fadi cikin wannan littafi nasu wani abu ne da ke nuni da asalin tushen wannan haramtacciyar kasar wacce ta ginu bisa kisan gilla da ayyukan ta'addanci.
1053216