IQNA

An Tarjama Littafin Diwanin Imam Khomeni (RA) A Cikin Harshen Bangala

Bangaren al'adu da fasaha, an tarjama littafin diwanin marigayi Imam Khomeini (RA) a cikin harshen Bangala daya daga cikin fitattun yaruka a yankin kudancin nahiyar Asia wanda karamin ofishin jakadancin jamhuriyar muslunci a birnin Daka ya dauki nauyin gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an tarjama littafin diwanin marigayi Imam Khomeini (RA) a cikin harshen Bangala daya daga cikin fitattun yaruka a yankin kudancin nahiyar Asia wanda karamin ofishin jakadancin jamhuriyar muslunci a birnin Daka ya dauki nauyin gudanarwa tare da bayar da makudan kudade wajen aiwatar da shirin.
Gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa a shirye take ta kirayi 'yan adawar Syria da nufin samar da hanyar da za ta kai su ga komaw akan teburin tattaunawa tare da gwamnatin kasar, da nufin kawo karshen rikicin da ake fama das hi.
A zantawar da ta hada shi da gidan talabijin din Al-alam a safiyar yau lhadi, ministan harkokin wajen Iran Ali Akbar Salihi ya bayyana cewa, za su kirayi 'yan adawar Syria domin su tatatuna tare da su, domin zaunar da su kan teburi guda da gwamnatin kasar, domin kuwa a cewarsa haka ne kawai hanyar warware rikicin kasar, domin kuwa ruruta rikicin Syria da kasashen turai ked a kuma aikewa da makamai da bama-bamai da mayaka da wasu kasashen larabawa ke hakan, hakan babu abin dazai jawo illa ci gaba da daidaita kasar, wanda hakan ne da dama kasashen turai suke bukata.
A bangare guda kuma wasu daga cikin 'yan ta'addan Syria da aka kame a kauyen Traisma sun fadi jiya agaban manema labarai cewa su ne suka yi kisan gilla kan fararen hula a kauyen da nufin jawo Karin matsin lamba kan gwamnatin Syria, kuma sun yi hakan ne a daidai lokacin kwamitin tsaron UN ke gudanar da zamansa kan Syria, ta yadda kai tsaye za a zargi sojojin Gwamnati da aikata hakan, kuma a cewar was daga cikinsu sun yi hakan ne tare da hadin baki da wasu kasashe da kuma wasu kafofin yada labarai, musamman Aljazeera mallakin gwamnatin Qatar da kuma Al-arabiyya.

1053297