IQNA

An Bude Wani Shafin Yanar Gizo Na Kur'ani Mai Tsarki A Kasar Turkiya

Bangaren fasaha da al'adu, an bude wani shafin sadarwa na yanar gizo kan ilmomin kur'ani mai tsarki a kasar turkiya da nufin kara watsa ilomin wannan littafi mai girma ga sauran al'ummomin duniya musamman wadanda suke magana ko fahimtar harshen turkanci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an bude wani shafin sadarwa na yanar gizo kan ilmomin kur'ani mai tsarki a kasar turkiya da nufin kara watsa ilomin wannan littafi mai girma ga sauran al'ummomin duniya musamman wadanda suke magana ko fahimtar harshen turkanci a cikin kasar da ma sauran kasashe.
Wasu rahotannin kuma sun yi nuni da cewa dubban mutanen birnin Istanbul na kasar Turkiya sun gudanar da wata gagagrumar zanga-zanga a birnin domin nuna rashin amincewarsu da matakan rashin imani da zalunci da mahukuntan kasashen Saudiyya da Bahrain suke dauka kan fararen hula masu neman sauyi ta hanyar lumana, daga ciki kuwa hard a aikin ta'addancin da suka yi kan malamin addinin nan na kasar a yankin Awamiyya da ke gabacin kasar.
Har wala yau a wani labarin na daban kuma day a shafi kasar an nuna cewa daruruwan 'ya kabilar kurdawa ne suka yi bata kashi tsakaninsu da 'yan sandan gwamnatin Turkiya a lokacin da suke gudanar da zanga-zanga a garin Diyar Bakar, domin neman a saki jagoran kungiyar Abdallah an da ake tsare da shi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan sandan gwamnatin Turkiya sun fada kan kurdawa fararen hula masu zanga-zanga a garin na Diyar Bakar, inda suka yi da dukarsu da kulake da kuma watsa musu ruwan zafi da hayaki mai sanya hawaye, lamarin da yayi sanadiyar jikkatar da dama daga cikinsu, daga ciki kuwa hard a wani dan majalisar dokokin kasar daga bangaren adawa da a shiga cikin zanga-zangar.
Kotun kasar Turkiya ta yanke hukuncin daurin rairai kan jagoran kungiyar 'yan awaren kurdawa ta Abdallah Aujalan a cikin shekara ta alif dari tara da casein da tara inda har yanzu ake ci gaba da tsare shi a gidan kaso.
1054624