Bangaren al’adu da fasaha, an gudanar da wani zaman taro kan muhimamncin kusanto da yarukan farisanci da kuma larabci a babban dakin gudanar da taruka nan a jamia’ar birnin Algiers na kasar Algeria wadda ta kasance daya daga cikin manyan jami’oin nahiyar Afirka.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, an gudanar da wani zaman taro kan muhimamncin kusanto da yarukan farisanci da kuma larabci a babban dakin gudanar da taruka nan a jamia’ar birnin Algiers na kasar Algeria wadda ta kasance daya daga cikin manyan jami’oin nahiyar Afirka da kuma na kasashen larabawa.
A dai dai lokacinda ake fara fitar da sakamakon zaben majalisar dokoki na farko wanda aka gudanar a kasar Libya bayan faduwar gwamnatin Mu'ammar Kazzafi, shugaban majalisar gwamnatin wucin gadi na kasar Mustafa Abduljalil ya bayyana cewa, da zarar cikekken sakamakon zaben majalisar dokokin kasar ya kammala, kuma sabuwar majalisar dokokin kasar ta yi zamanta na farko, zai rusa majalisar gwamnatin wucin gadin kasar ya kuma mika ragamar jagorancin kasar ga sabuwar majalisar.
Ya zuwa yanzu dai sakamakon zaben ya na nuna cewa gamayyar jam'iyyu masu kishin kasa karkashin jagorancin Mahmood Jibril ne suka sami galaba a galibin mazabun babban birnin kasar wato Tripoli da kuma gewayensa, hukumar zaben kasar ta Libya mai cin gashin kanta, ta bayyana gamayar kananan jam'iyyu kimani 60 karkashin jagorancin Mahmood Jibril ne suke kan gaba tare da kuri'u dubu 46 a birnin Tripoli, a yayinda jam'iyyar Adalci da gina kasa, ta yan uwa musulmi ko (ikhwanul- muslimin) ta sami kuri'u dubu 4 kacal mazabun babban birnin kasar.
Sabuwar majalisar dokokin kasar ta Libya dai zata kasance mai kujeru 200 ne, kuma ana saran mafi rinjayen kujerun zasu shiga hannun yan takara masu zaman kansu ne. Don haka har yanzun dai ba za'a iya hasashen jam'iyyar da zata sami rinjaye a majalisar ba.
Mustafa Abduljalil shugaban majalisar gwamnatin rikon koriya ta kasar ya bayyana cewa, majalisar tana goyon bayan ra'ayin jama'a don haka ne ta kuduri anniyar ya mika ragamar ikon kasar ga sabuwar majalisar, da zarar ta fara zama. Ya ce tana da damar tabbatarwa ko kora, ko kuma yin koskorima wa dukkan dokokin da majalisarsa ta wucin gadi ta kafa.
1055478