IQNA

Yankin gabas Ta Tsakiya Ya Zama Babbar Cibiya Ta Rikice-Rikice

Bangaren al’adu da ilimi, yankin gabas ta tsakiya ya zama wata bababr madadala ta riki a yankin da ke samun iza wuta daga manyan kasashen duniya da suke fatan ganin sun murkushe musulmi ko ta wace hanya domin su awwashe arzikinsu kuma tabbatar da ikonsu da bayar da kariya ga yar lelansu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a halin yanzu dai yankin gabas ta tsakiya ya zama wata bababr madadala ta riki a yankin da ke samun iza wuta daga manyan kasashen duniya da suke fatan ganin sun murkushe musulmi ko ta wace hanya domin su awwashe arzikinsu kuma tabbatar da ikonsu da bayar da kariya ga yar lelansu haramtacciyar kasar yahudawan sahyuniya.
Shugaban kasar Syria Dr Bashar al-asad ya nada Janar Fahd Al-jassen alfreij a matsayin ministan tsaro a yau laraba jim kadan bayan mutuwar ministan tsaron kasar a wani harin bom da aka kai a ginin ma'aikatar tsaron kasar a safiyar yau din, ministan tsaron kasar ta Syria Janar Dawood Rajiha da kuma mataimakinsa Assef Shawkat duk sun rasa rayukansu a wannan harin, a dai dai lokacinda suke taro a cikin ginin.

Gidan television na gwamnatin kasar Syria ya bayyana da cewa akwai wasu jami'an gwamnatin kasar da dama wadanda suka ji rauni a wannan harin, daga cikinsu akwai ministan cikin gida Major General Mohammad Ibrahim al-Sha'ar, har'ila yau bayanin ya kara da cewa mai yuwa a kara samun wadanda zasu rasa rayukansu sanadiyyar raunuka da suka samu.

Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da harin da ya halaka jami'an tsaron kasar ta Syria. Ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Akbar Salih ya yi Magana ta wayar tarho da tokworansa na kasar Syria Walid al-Mu'allim inda ya gabatar da ta'aziyyarsa ga dangin wadanda suka rasa rayukansu da kuma mutanenn kasar Syria.

1056812