Bangaren fikira, nan ba da jimawa za a gudanar wani zaman taro a kasar Ivory Coast dangane da fikirar mahdawiyya kamar dai yadda ake kallonta a mahangar tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka wanda kuma malamai ne za su gabatar da jawabansu a gaban taron.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na jami’ar mostafa, cewa nan ba da jimawa za a gudanar wani zaman taro a kasar Ivory Coast dangane da fikirar mahdawiyya kamar dai yadda ake kallonta a mahangar tafarkin iyalan gidan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka wanda kuma malamai ne za su gabatar da jawabansu a gaban taron kamar dai yadda akasanar.
A wani labarin kumada ya shafi kasar kungiyoyin fararen hula da 'yan siyasa a Ivory Coast sun bayyana damuwarsu kan matsalar tashe tashen hankulan da suke ci gaba da wanzuwa a kasar. A bayanin da gamayyar kungiyoyin fararen hulan kasar Ivory Coast ta fitar yana dauke da nuna takaici da tsananin damuwa kan yadda matakan tsaro suke kara tabarbarewa a kasar ta Ivory Coast musamman rikicin kabilanci da kuma ci gaba da yaduwan makamai a hannun jama'a. Har ila yau wasu manyan 'yan siyasar Ivory Coast sun koka kan matsalar tashe tashen hankul a kasar musamman yin garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran muggan ayyukan ta'addanci da suke firgita jama'a a kullum rana.
A ranakun lahadi da litinin da suka gabata ma wasu mahara sun kai hare hare kan ofishin 'yan sanda, wajen binciken ababawan hawa da sansanin sojin Ivory Coast da suke birnin Abidjan cibiyar kasuwancin kasar, inda hare haren suka lashe rayukan sojojin fiye da goma kamar dai yadda majiyoyin rundunar sojin kasar da mahuunta suka tabbatar.
1073792